FATAWA 8 = HUKUNCIN RATAYA LAYA DA GURU.

HUKUNCIN RATAYA LAYA DA GURU !!!!

Tambaya:

Assalam Alaikum.Malam, menene hukuncin amfani da laya ko guru a musulunci?
Allah yasa mu dace.
Amsa:
Wa alaikum assalam,To ]an’uwa Layu da guru sun kasu kashi biyu:
1. Layun da aka yi su da Sa}andami ko Hatimi ko sunayan aljanu ko wani abu na
daban wanda ba Qur'ani ba, wannnan malamai sun cimma daidaito game da
haramcinsu kamar yadda ya zo a Fataawaa Allajna Adda'imah 1/212 saboda fa]in
Annabi tsira da amincin allah su tabbata a gare shi (layu da kuma abin da ake
]aurawa mace don miji ya so ta shirka ne) kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a
hadisi mai lamba ta: (3883) kuma Albani ya inganta shi, sannan da hadisin da
Imamu Ahmad ya rawaito mai lamba ta: (16969), inda Annabi tsira da amincin
allah su tabbata a gare shi yake cewa: (Wanda ya rataya laya to ya yi shirka), shima
wannnan hadisin Albani ya inganta shi a Silsila Sahiha.hakan sai ya nuna haramcin
]aura Laya saboda Manzon tsira ya kira ta da shirka, shirka kuma tana fitar da
mutum daga musulunci.
2. LAYUN da aka yi su daga Alqur'ani ko hadisai ingantattu, wadannan na'u'i
malamai sun yi sa~ani akansu:
A. Sun halatta saboda sun }unshi sunan Allah da kuma karatun alqur'ani wanda
sifar Allah ce, wanda ya dogara da su ya dogara ga Allah, wannan ita ce maganar
Amru bn Al-ass da Aisha da wasu daga cikin magabata. B. Ba su halatta ba saboda ba'a samu Annabi tsira da amincin allah su tabbata a
gare shi ya yi ba, da hakan sharia ne da an gan shi ya yi ko da sau ]aya ne a
rayuwarshi, sannan rataya layun da suke ]auke da Alqur'ani zai jawo a wula}anta
su tun da za'a shiga wurare marasa tsarki da su lokacin biyan bu}ata, kiyaye hakan
kuma yana da kamar wuya.
Zance mafi inganci shi ne haramcin amfani da Layun da suke daga Alqur'ani
saboda dukkan alkairi yana cikin biyayya ga manzon Allah tsira da amincin allah
su tabbata a gare shi, sannan shariar musulunci ta halatta mana addu'o'i da yawa na
neman kariya wa]anda suka wadatar da mu daga layu. Allah ne mafi sani.
Dr jamilu zarewa A.b.u

Post a Comment

0 Comments

ads1