Sallar Matafiyi (Qasaru)
Anshar’antawa matafiyi yin qasarun sallloli masu raka’a hudu (Azzahar,La’asar,Isha)zuwa
raka’a biyu, haka kuma zai iya hada
sallar azzahar da la’asar,margariba da isha,saboda fadin Allah
Madaukakin Sarki:
"(Idan kukayi tafiya a bayan qasa to babu laifi akanku ku rage(qasaru)sallah, in kuna jin tsoron
kada wadanda suka kafirta sufitineku, haqiqa kafirai maqiyan kune masu bayyana qiyayya)"
@Anni sa’i aya ta101.
Da abin daya tabbata daga Anas Dan Malik–Allah ya yarda dashi–yace,*“Mun fita tare da
Manzon Allah(ملسوهيلعهللاىلص)daga Madinah zuwa Makkah, ya kasance
yana mana sallah raka’a bibiyu, har muka dawo”*
@Nasa’ine ya rawaitoshi.
Abin Da Ake Nufi Da Tafiya
*"Itace duk tafiyarda za'a kirawota tafiya a al’adance, to wannan tafiya za'ayi mata qasaru*
Sallar Qasaru
1–Matafiyi zai fara qasaru daya bar gidajen garinsu. Baya halatta yayi qasaru acikin gidan da
yake zaune, saboda bai tabbata Manzon Allah(ملسوهيلعهللاىلص)yayi qasaru ba har sai bayan
ya fita (daga gari).
2–Matafiyi ya isa wani gari, kuma yayi niyyar zama kwana hudu ko sama da haka, to zaici
gaba ne da kasaru har sai ya dawo gida, idan kuwa bai niyyar wasu kwanaki qididdi gagguba,
kawai dai yana da wata buqatace, duk lokacin daya qareta zai koma, to wannan ya halatta yayi
ta qasaru har sai yadawo, koda kuwa lokacin yawuce kwana hudu. wannan itace magana mafii nganci.
3–Wajibi matafiyi ya cika sallah idan yayi sallah bayan liman mazaunin gida, koda kuwa raka’a
daya ya samu atare dashi.
4–Idan mazaunin gida yayi sallah bayan matafiyin da yake qasaru, to wajibine akansa ya cika
sallah bayan liman yayi sallama.
Hada Salloli Biyu
1–Ya halatta matafiyi da mara lafiya su hada salloli biyu, azzahar da la’asar alokacin daya daga
cikinsu, magariba da isha alokacin daya daga cikinsu. Idan ya hada sallar ne alokacin ta farko, to
wannan shine *“Jam’uTaqdim”*, in kuwa yaha daa lokacin sallah ta biyu,to wannan shine
*“Jam’uTa’akhir”*
2–Ya halatta ga wanda yayi sallah a masallaci ya hada sallah saboda ruwan samanda zaisha
wahala da qunci(wajen dawowa masallaci acikinsa).
Amma wanda yake yin sallah acikin
gidansa, kamar mata,ba'ayi musu rangwamen hada sallah ba.
3–Ba dole bane qasaru da hada sallah biyu su hadu alokaci guda ba, za 'a iya hadawa ba tare
da qasaru ba, za'a kuma iya yin qasaru batare da hada waba.
Sallar Matafiyi ACikin Mota
1–Idan sallar nafilace ta inganta da uzuri ko ba uzuri, saboda abinda ya tabbata cewa
*“Manzon Allah SAW
ya kasance yana yin sallar nafila akan abin hawansa, dukin da abin hawan yayi dashi”*
@Bukhari ne ya rawaitoshi.
2–Idan kuwa sallar farillace tana inganta idan yakasance baya iya sauka kan qasa, kokuma ba
zai iya hawa ba idan ya sauka, kokuma yana jin tsoron abokin gaba, da makamancin haka.
Sallar anan tana da kamanni dayawa, daga cikinsu akwai:
*A–Yazama zai iya fuskantar alqibla, kuma zai iya ruku’u da sujjada, kamar ace yana cikin jirgin
ruwa, to anan wajibine yayi sallah yadda take,saboda zai iyayi.
*B–Ya zama zai iya fuskantar alqibla, amma ba zai iya ruku’u da sujjada ba, to wajibine ya
fuskanci alqiblar yayin kabbarar harama, sannan yaci gaba da sallar duk inda motar tayi da
shi, yana mai nuni wajen ruku’un sa da sujjadarsa.
Allah ne mafi sani.
0 Comments