YADDA AKE WARWARE SIHIRI
Tambaya:


Assalamu alaikum Dan Allah malam a fitar dani cikin duhu game da abin da yake
damuna Mahaifiya ta ce ta je gurin malami ai mata maganin ciwon mara da yake
damunta, tace tana da ciki yakai shekara, amma likitoci sun yi scanning sunce ba
komai to sai malamin ya ce mata asiri aka yi mata, kuma zai yi mata magani nan
take ta haife abinda yake cikinta amma za ta kawo tunkiya da dubu bakwai, sai
take min magana in kawo ku]i a sayi tunkiyar kuma akai masa dubu bakwan, to
gaskiya malam zuciyata ba ta aminta da malaman ba ne shi yasa ! Na keso ka bani
fatawa shin irin wannan hanyar ta magani ta halatta a addini? Idan bata halatta ba
wacce hanya zan bi wajen qin biyan ku]in da kuma sanar da ita, saboda ina da
matsala , ta ~angaren aqeeda mun banbanta? Wassalam na gode malam Allah Ya
qara basira


Amsa:

To 'yar'uwa tabbas ba a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware
sihiri ta hanyar ayoyin Alqur'ani, wasu malaman sun yi bayani cewa : ana iya
warware sihiri ta hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da
Nasi, da kuma aya ta : 117 zuwa ta 122, na suratul A'araf, sai kuma aya ta : 79-81 a
suratu Yunus, sannan sai a hada da aya ta : 65-70 a suratu Dhaha, za'a karanta su,
sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai, sannan ayi wanka da shi .
Bai halatta ki taimaka mata ba wajan bada wadannan kayan da boka ya nema,
saboda ba'a yiwa iyaye biyayya a wajen sa~on Allah, ya wajaba ki yi mata nasiha
cikin hikima, ki sanar da ita cewa : Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi yana cewa : "Duk wanda ya je wajan boka, ya tambaye shi wani abu, Allah ba
zai amshi sallarsa ba ta kawana arba'in" kamar yadda muslim ya rawaito a hadisi
mai lamba ta : 2230, Kin ga in mutum ya mutu a wadannan kwanaki akwai
matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari'a ta yarda da ita, a wani
hadisin kuma yana cewa : "Duk wanda ya je wajan boka ya gaskata abin da ya
fada, to tabbas ya kafurce da abin da annabi Muhammad ya zo da shi" kamar yadda
ya zo a Sunanu-abi-dawud hadisi mai lamba ta : 3904, kuma Albani ya inganta shi
.Ina ganin da irin wadannan hadisan za ki iya ganar da ita, ta dawo kan hanya.
Allah ne mafi sani .

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
AHMADU BELLO UNIVERSITY,
ZARIA.