HUKUNCIN FIDDA'U (SAUKEWA MAMACI ALQUR'ANI
BAYAN YA MUTU)

Tambaya:
Assalamu alaikum. Wai malam Meye Hukuncin Saukewa Mamaci Al-qur'ani?

Amsa:

Wa alaikum assalam, To malamai sun yi sa~ani akan wannan mas'ala zuwa
maganganu guda uku:
1. Bai halatta ba, saboda ba'a samu wani nassi da yake nuni zuwa haka ba, kuma
ita ibada ba'a yinta sai da nassi na musamman, sannan kuma mutum ba shi da wani
abu sai aikinsa, kamar yadda aya ta 39 da take cikin suratu Najm, take nuni zuwa
haka, tun da ba'a samu ba, yin hakan zai zama bidi'a, wannan ita ce maganar
Shafi'i.
2. Ya halatta a yi, saboda hadisan da suke nuna cewa mamacin yana iya amfana da
abin da mai rai zai masa, kamar hadisan da suka yi umarni da yi masa sallah da
nema masa gafara bayan ya mutu, da yi masa sada}a, wannan shi ne maganar mafi
yawan malamai, har wasu marubuta ma sun hakaito ijma'i akan haka, saboda
mutane sun jima suna yi kuma malamai ba su yi musu inkari ba.
3. Akwai wa]anda suka tafi akan cewa idan dansa na cikinsa ya yi masa, to ladan
zai same shi, amma wanda ba dansa ba, ba zai yi masa ba, saboda fa]in Annabi
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi "Dan mutum yana daga cikin aikinsa"
Abudawud ya rawaito shi kuma Albani ya inganta shi a sahihu sunani-Abi-Dawud
hadisi mai lamba ta: 2528.
Wasu malaman, suna rinjayar da magana ta uku, saboda fa]in Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi: "Idan ]an'adam ya rasu ayyukansa sukan
yanke sai ]ayan abubuwa guda uku: sada}a mai gudana, ko ilimin da ake amfana
da shi, ko ]a nagari da yake masa addu'a" kamar yadda Tirmizi ya rawaito shi kuma ya
inganta shi a hadisi mai lamba ta: 1376, Wa]ancan hadisan kuwa da masu magana ta biyu
suka }afa hujja da su, to za'a yi amfani da su ne a iya inda suka zo, amma ba za'a yi
kiyasin karatun qur'ani akan su ba.
Don neman }arin bayani, a duba Majmu'ul fataawa:24\366 da Nailul Audaar 4\112
da Ahakamul jana'iz shafi na: 171. Allah ne ma fi sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
AHMADU BELLO UNIVERSITY,
ZARIA