FATAWA 3 = HUKUNCIN ZAMAN MAKOKI.

HUKUNCIN ZAMAN MAKOKI
Tambaya:

Malam mahaifina ya rasu, sai wani malamin islamiyyarmu ya ce min ba kyau
zaman makoki, to gaskiya kaina ya daure, saboda na taso na ga ana yi, kuma idan
ban yi ba za'a ce ban damu da mahifinmu ba, malam yanzu yaya zan yi ? Allah Ya
datar da kai zuwa dukkan alkairai .

Amsa:

To ]an’uwa Allah Ya ba mu dacewa gaba ]aya, tabbas malamai sun tattauna akan
hukuncin zaman makoki, saidai sun kasu kashi uku :
1. Akwai wa]anda suka tafi akan makaruhi ne, saboda hadisin Jarir RA wanda
Imamu Ahmad ya rawaito cewa: "Mun kasance muna
}irga taruwa yayin mutuwa da kuma yin abinci a gidan da aka yi mutuwa daga
cikin rurin da Allah da ya haramta" , Musnad : 6905, don haka suna cewa, saidai a
ha]u da wa]anda aka yiwa rasuwa akan hanya ko a kasuwa, ko masallaci ayi musu
ta'aziyya, wannan ita ce maganar Shafi'i a cikin Umm 1\318, haka Nawawy a
Majmu'u 3\306 .
2. Akwai wa]anda suka ta tafi akan cewa bidi'a ne, kamar Ibnul-kayyim a zadul
ma'ad 1\527.
3. Akwai malaman da suka tafi akan halaccin zaman makoki, saboda hadisin da
nana A'isha ta rawaito cewa, lokacin da aka kashe Zaid dan Haritha da Ja'afar dan
Abu-dalib Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya zauna a wani
wuri, duk wanda ya gan shi zai ga alamun bakin ciki tare da shi, sai wani mutum
ya zo ya ce masa : ga matan Ja'afar can suna ta kuka, sai Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya umarce shi da ya je ya hana su, su kuma yi ha}uri"
Bukhari hadisi mai lamba ta : 1299, wadannan malaman suna cewa : Za'a iya
fahimtar hallacin zaman makoki a wannan hadisin a wurare guda biyu.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
AHMADU BELLO UNIVERSITY,
ZARIA

Post a Comment

0 Comments

ads1