Assalam

Kamar yadda kuka sani subtitle shine wannan Rubutun dayake fitowa yayin da muke kallon film/video wannan Rubutun dayake fitowa da zarar anyi magana acikin film din sai a Rubutu maganar daga kasa to wannan shine subtitle
To kaima zaka iya hada naka Subtitle din da kanka da farko ka tabbata kana da Root Explore kokuma wata Explore da ban,
Sannan saika bude explore dinka kaje folder da babu kome sanna ka budeta idan ta dube zakaga wasu abubuwa daga kasa to saika danna alamar plus + idan ka danna zakaga wasu Rubutu to kawai ka shiga inda aka Rubuta
File
Da zarar ka shiga zai nunama inda zaka Rubuta sunan da zaka sawa Subtitle din naka to anan saika Rubuta sunan subtitle din sannan ka kara format din .srt misali kamar haka subtitle1.srt
Bayan kun Rubuta sai kuyi save sannan zakuga File din naku a wannan folder, to yanzu abin da zakuyi kawai kudan danne shi da hannunku zai nuno muku wasu rubutu to saiku shiga inda aka Rubuta Open in Text Editor saiku shiga nan to anan ne gun da zaku Rubuta Subtitle dinku,
To yadda zakuyi shine saiku fara rubuta subtitle din naku ga yadda zaku Rubuta
Da farko saku fara sa number subtitle din ita kuma number tana farawa daga 1 zuwa karshen yadda Film din zai kare sannan ajere akesa number idan kasa number ta farko to saika Rubuta iya maganar da take gun sannan magana ta biyu kuma saiku sata a number ta 2 haka magana ta uku a number 3 sannan tsakanin kowace magana sai kunyi sakin layi haka abin yake
Sannan kuma abin yana farawa daga Hours na film din da kuma Minti sannan da second haka abin yake
wato zuku tsarashi kamar haka

1 00:00:05,199 - -> 00:00:50,500 saiku rubutu maganar data faru a farko daga second 5 zuwa secon 50 iya inda film din naka yake haka zaka rubuta abinka sannan sai kayi sakin layi kasa number 2 sannan kayi kamar yadda nayi na farko amma saika setta secon ko minti sannan daga kasa kayi rubutun da aka fada acikin film din
2 00:00:56,600 - -> 00:00:59,725 Sai maganar da akayi a wannan lokacin anan
3 00:01:00,350 - -> 00:01:02,058 saika rubuta magana anan
4 00:01:02,850 - -> 00:01:07,392 Saika Rubuta magana anan

Shikkenan haka zakayi tayi har sai kakai karshen film din Idan ka hada sai kayi save sannan ka fito shikkenan ka gama hada subtitle sai kaje ka dorashi akan film din daka hada naka domin dorawar saikayi amfani da MX PLAYER wajen dorawar, idan ka budeta ka kamo film din da kake kallo saika danna menu zakaga Subtitle saika shiga nan zata kawoka kan wayarka ko memory sai kaje folder daka hadashi sai kayi click akansa shikkenan
Insha Allah zakaga ya hau
Allah ya bada sa,a

@J EX- BRD