NA TSINCI NAIRA N5,00 KO ZAN IYA AMFANI DA ITA BA TARE
DA CIGIYA BA ?
Tambaya:
Wani bawan Allah ne ya tsinci Naira: #500, a wurin kuma bai ga wa]anda zai yi
wa cikiya ba... Ya ya kamata yayi da ku]in tsintuwar ?, suna ajiye yanzu haka
kusan wata ]aya .
Amsa:
.. To ]an’uwa idan mutum ya yi tsintuwa ya wajaba a gare shi ya yi cigiya har
tsawon shekara guda, idan bai samu mai ita ba, daga nan zai iya amfani da ita,
amma in mai ita ya zo daga baya zai biya shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a
hadisi mai lamba ta: 5761.
Amma idan abin da ya tsinta dan ka]an ne ba shi da yawa, to ya halatta ya yi
amfani da shi ko da bai yi cigiya ba, saboda abin da aka rawaito cewa : Annabi
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ga wani ]abino akan hanya, sai yace : In ban da ına tsoron na sada}a ne da na ci. Muslim ya rawaito a lamba ta:
2527, sai hadi in ya nuna dan }aramin abu ba ya bu}atar cigiya, Malamai un yi
sa~ani wajan iyakance tsintuwar da ba ta bu}atar cigiya, wasu sun ce za'a koma
al'adar mutane, duk abin da mutane uke ganinsa ba a bakin komai ba, to in an
tsince shi ba ya bu}atar cigiya, Ibnu Khudama ya hakaito daga Imamu Malik cewa:
bai wajaba mutum ya yi cigiyar abin da bai kai a yanke hannu saboda shi ba, wato
]aya bisa hu]un dinari, haka nan sayyadina Aliyu ya tsinci dinare ]aya ya yi
amfani da ita ba tare da yayi cigiya ba. Abin da ya gabata yana nuna cewa:
mutu}ar ba ka samu mai Naira (5,00) din da ka tsinta ba a kusa da Kai, ya halatta
ka yi amfani da ita ba tare da cigiya ba, tun ba ku]i ne mai yawa ba, kuma mai ita
ba zai kwallafa rai Akanta ba. Don neman }arin bayani duba : Al-mugni 6/351.
Allah ne mafi Sani
0 Comments