HUKUNCIN WASAN KWALLON KAFA ! !
Tambaya:
Malam ina tambaya ne akan kwallon qafa, a kwai wanda yake neman aurena
sana'arsa kenan, da ita yake ci yake sha yake komai, so malam ina kokonto akan
wannar sana'ar tasa, kada ya kasance sai anyi auren in ji cewa ba halal bane, tunda
ana biyansa idan suka yi wasa, to shine malam ko a taqaice a sanar dani wani abu
akai, saboda mu san makamar mu, nagode•
Amsa:
To 'yar'uwa ına ro}on Allah Ya baki miji nagari, malamai suna kasa }wallo gıda
uku :
1. Kwallon da ake yi saboda motsa jiki, kamar mutum biyu su ha]u, su
yi ball don su tsinka jinin jikinsu, wannan kam ta hallata mutu}ar ba ta
kautar daga ambaton Allah ba, ko kuma sallah idan lokacinta ya shiga .
2. Kwallon da kungiyoyi biyu ko sama da haka za su ha]a ku]i su sayı
kofi wanda a }arshe kungiya ]aya za ta ]auka, wannan kam bai halatta ba,
saboda daidai yake da CACA, kuma yana sabbaba gaba da kiyayya a
tsakanin 'yan kwallo.
3. Idan ya zama wani ne daban zai sanya Kofin, shi ma malamai sun ce
haramun ne saboda asali musabaka da wasan tsere haramun ne, in ba abin da
dalili na shari'a ya halatta ba, irin wannan kwallon kuma ba ta cikin abin da
aka togace, sannan akwai ~arna mai yawa a cikinta, domin zai yi wuya a
tashi irin wannan Kwallon wani bai ji ciwo ko ya karye ba, ga kuma haushi
da kulewa da yake samun wanda aka kayar, wasu lokutan har da doke-doke
tsakanin }ungiyoyin guda biyu.
Idan ya zama mijin da za ki aura yana yın nau'i na na biyu ko na uku, to ya
wajaba ki yi masa nasiha idan kuma yaki ji, to auransa akwai ha]ari saboda zai ciyar dake da haramun. Don neman }arin bayani duba Fataawaa Al-lajna
Adda'imah 3/238 da kuma Fataawaa Muhammad bn Ibrahim 8/116.
Allah ne mafi Sani.
0 Comments