ZAN IYA JAN CARBI, KO KO BIDI'A NE.
Tambaya?
Assalamu Alaikum. Tambaya. Allah ya gafartawa Malam Na kasance ina amfani
da charbi (Tasbaha) domin yana tunatar dani wajen ambaton Allah a kowane
lokaci. Ina matsayin haka a sharia ?
Amsa:
Wa'alaykumussalam, To ]an'uwa jan carbi ba bidi'a ba ne, saboda duk da cewa
babu shi a zamanin Annabi s.a.w. hakan ba zai sa ya zama bidi'a ba, saboda wanda
yake amfani da shi ba ya nufin cewa ibada ce mai zaman kanta, yana amfani da shi
ne, don ya kiyaye adadin zikirinsa.
Yin amfani da 'yan yatsu shi ne yafi, saboda hadisi ya yi nuni cewa : za'a ba su
dama su yi magana ranar alkiyama, kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma Albani
ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: 3486, don haka za su yi maka shaidar abin da
ka yi na alkairi, sa~anin carbi, Sannan sau da yawa za ka ga mutum yana jan carbi
amma hankalisa yana wani wajen, sa~anin idan da hannu yake yi, Jan carbi yakan
iya sanya wasu su yi riya, saboda wasu suna ratayawa ne a wuya don a gane su
zakirai ne.
Annabi s.aw. yana yin tasbihi da hannunsa na dama kamar yadda ya tabbata a
hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 1286, wanda Albani ya inganta, saidai wasu
malaman suna cewa in ya yi da hagu ma yayi, tare da cewa yi da dama shi ne yafi.
Saidai duk da dalilan da suka gabata, mutum zai iya jan carbinsa, tun da jan carbib ba ibada ce mai zaman kanta ba, balle ace ya zama bidi'a, ga shi kuma ba'a samu
wani hadisi da ya hana ba, tare da cewa yi da hannu shi ne yafi, Don neman Karin
bayani duba : Majmu'ul fataawa 22\187. da Lika'ul maftuh na Ibnu-uthaimin 3\30.
0 Comments