CIN NAMAN DOKI HALAL NE


Tambaya:
Assalamu Alaikum dan Allah tambayar ita ce shin akwai wani hadith ko Aya
wacce ta nuna cewa cin naman doki haramun ne?


Amsa :

To ]an’uwa babu wata aya baro-baro ko wani hadisi wanda ya haramta cin naman
doki, kuma mafi yawan malamai sun tafi akan hallacin cin naman doki, saboda
hadisin Asma'u 'yar Abubakar, inda take cewa : "Mun soke wani doki a zamanin
annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai muka cinye shi" Bukhari :
(5191) Saidai Ibnu Abbas da Imamu Malik sun tafi akan haramcinsa, saboda Allah
Ya fada a cikin suratu Annahl aya ta : 8 cewa ya halicci doki ne don a hau, a kuma
yi ado, wannan sai yake nuna ba za'a ci ba.
Zance mafi inganci shi ne hallacin cin naman doki, saboda hadisin da ya gabata,
sannan ayar da Imamu Malik ya }afa hujja da ita ba ta fito baro-baro ta hana cin
doki ba, domin kasancewar an ce ana hawansa ko ana ado da shi, ba ya hana a ci .
Don neman }arin bayani duba tafsirin Kurdubi 10\68.
Allah ne mafi sani.