Sauyi takwas da Yariman Saudiyya ya kawo a bangaren nishadi.

Sauyi takwas da Yariman Saudiyya ya kawo a bangaren nishadi

Yariman SaudiyyaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Tun bayan da aka sanar da zuwan mawakiya Nicki Minaj Saudiyya domin yin waka, sai kafafen sada zumuntar kasar suka rude da ce-ce-ku-ce kan batun.
Ana sa ran Nicki Minaj za ta je kasar ne ranar 18 ga watan Yuli a wajen taron raye-raye na shekara-shekara wato Jeddah World Fest.
Duk da cewa wannan ba shi ne karo na farko da aka samu irin wannan sauyin ba, ana nuna damuwa kan zuwan Minaj ne musamman ganin irin shigar da mawakiyar ke yi a lokacin da take waka, a kuma kasar da ake yi wa kallon 'mai tsaurin ra'ayi'.

Ana ganin cewa Yarima Mohammed bin Salman mai jiran gado ne ke kawo wadannan sauye-sauye a kasar musamman a bangaren nishadantarwa.
A watan Fabrairun 2018 ne Saudiyya ta ce za ta ware kudi dala biliyan 64 domin bunkasa masana'antunta na nishadantarwa a cikin shekaru 10 masu zuwa.
Shugaban hukumar da ke kula da harkokin nishadi a kasar ya ce an tsara shirya abubuwa kimanin 5,000 a bara kawai da suka kunshi har da bikin cashewa na Maroon 5 kamar irin wanda ake gudanarwa a Amurka.
Shirin zuba jarin na cikin sabbin manufofin bunkasa tattalin arziki da ake kira Vision 2030 wanda Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya kaddamar shekaru biyu da suka gaba.
sinima saudiyyaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Kafofin yada labaran Saudiyya sun ambato Ahmed bin Aqeel al-Khatib shugaban hukumar harakokin nishadi yana cewa, yana fatan za su dauki mutum 220,000 aiki a bangaren nishadi kafin karshen 2018.
Yarima Mohammed bin Salman ya ayyana kudirinsa cewa yana son mayar da Saudiyya "matsayin kasa mai sassaucin ra'ayin addini tare da bude kofa ga dukkanin addinai da al'adu da mutanen duniya".
Ga dai jerin wasu sauye-sauye da yariman ya kawo a bangaren nishadantarwa a kasar:
Wannan layi ne

Dage haramci kan sinima

A watan Disambar 2018 ne, gwamnatin Saudiya ta dage haramci kan gidajen sinima.
Tuni dai Saudiyyar ta sanar da bayar da damar bude gidajen nuna fina-finai a kasar.
Short presentational grey line

Tarukan casu

Tawagar mawaka ta Cirque Éloize ce ta farko da suka yi casu a watan Janairun 2018 wanda shi ne karon farko a birnin Dammam na Saudiyya.
Bikin casu na Cirque du Soleil irin wanda ake gudanarwa a kasashen Turai. Tuni dai Saudiyya ta fara aikin gina wajen casu a birnin Riyadh.
Haka kuma kasar ta sanar da cewa za ta gayyaci mawaka irin su Jay Z da Mariah Carey da kuma taurarin 'yan kwallo irin su David Beckham.
Short presentational grey line
Dage haramcin tuki ga mata
Wata mata tana tuka motaHakkin mallakar hotoAFP/GETTY
Image captionKafain wannan lokaci sai dai a yi hayar direba ya tuka mata a mota
A watan Satumbar 2018 ne gwamnatin Saudiyya ta sanar da dage haramcin tuki ga mata, kuma tuni aka fara bai wa matan lasisin tuki a Saudiyya.
Kafin dage haramcin Saudiyya ta kasance kasa ta karshe a duniya da mata ba su da izinin yin tuki.
Sai dai duk da wannan ci gaban ga matan Saudiyya, ana zargin hukumomin kasar da bin matakai na murkushe wadanda suka yi gwagwarmayar tabbatar da ba mata 'yancin tuki a kasar.
Short presentational grey line

Bude gidan rawa a Saudiyya

Gidan rawaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionYawanci an fi samun gidajen rawa a kasashen Turawa
Kazalika, a watan Yunin 2019 wani gidan rawa na birnbin Dubai a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa mai suna White ya sanar da bude sabon gidan rawar da ya kira "Halal Disco" a Jiddah.
Kafofin yada labarai na kasar sun tabbatar da bude gidan rawar wanda suka ce tsarinsa ya yi kama sosai da gidan casu na dare da aka sani, sai dai kuma ba za a dinga shan barasa a wajen ba.
Shi ma gidan rawar na White ya ce wurin zai yi kama ne da dakin hira ba da mashaya ba.
Short presentational grey line

Bikin kafa Saudiyya da ya kawo gwamutsa mata da maza

Mata a wurin taron 'yancin kan SaudiyyaHakkin mallakar hotoREUTERS
Image captionAna iya ganin maza da mata a cakude a yayin bikin
A karon farko an ba mata damar shiga wani filin wasanni don bikin zagayowar ranar 'yancin kan Masarautar Saudiyya.
A watan Satumbar 2017 ne filin wasa na Sarki Fahad a Riyadh babban birnin ƙasar, ya maƙare da ɗaruruwan matan da suka yi ɗango don cin wannan gajiya.
An ga mata a wasu lokuta ma cakuÉ—e da maza a kan kujeru suna karkaÉ—a tutocin Saudiyya albarkacin murnar ranar kafa Saudiyya.
Rahotanni sun ce bukukuwan wani yunkuri ne na gwamnatin Sarki Salman don yaukaka alfahari da kasa da kuma inganta matsayin rayuwar Sa'udi.
A wannan mako ne, Saudiyya ke shagulgulan cika shekara 87 da kafuwarta a matsayin ƙasa.
Short presentational grey line
Kallon 'yan kokawa na Amurka
Kokawar rislinHakkin mallakar hotoAFP
Image captionAna son kokawar Turawa a Gabas ta Tsakiya
A karon farko a watan Afrilun 2018 an bai wa mata da maza damar shiga kallon wasan kokawa na Turawan Amurka wato wrestling.
An gudanar da damben kokawar na (WWE) a birnin Jiddah, kuma maza da mata ne suka shiga kallo wanda kafar telebijin din kasar ta nuna kai tsaye.
Maza zalla ne suka fafata a kokawar a Saudiya yayin da aka haramta damben mata a kasar.
Sai dai a yayin da mutane ke tsaka da kallon kokawar sai ga tallar damben mata suna gani sanye da kamfai da kananan riguna kamar yadda suka saba yin damben nasu.
Gwamnatin Saudiyyar dai ta nemi gafara sakamakon kutsen da hoton bidiyon mata 'yan kokawar ya yi.
Short presentational grey line

Shigar mata wajen kallon kwallo

Wasu mata kenan a wurin kallon kwallon kafaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMatan Saudia sun samu 'yancin shiga filayen wasanni don kallon wasan kwallon kafa da sauransu
Kamfannin dillancin labaran kasar ne ya sanar da cewa daga yanzu za a rinka barin iyalan mutum da suka hada da mata da yara su rinka halartar filayen wasanni da ke manyan biranen kasar uku, wato na Riyadh da Jedda da kuma Dammam.
Wannan sabon mataki dai ya fara aiki ne daga farkon shekarar 2018.
Hakan dai wata 'yar dama ce a masauratar da ake killace mata a gidaje, domin a kara fito da su don shiga a dama da su a cikin al'umma.
Short presentational grey line
Tseren keken mata zalla
Wasu mata masu tseren kekunaHakkin mallakar hotoINSTAGRAM/@JEDDAH_WOMAN
Image captionMasu tseren keke sun shirya tsaf don tseren keke ta mata ta farko a Saudi Arabia
A watan Afrilun 2018 ne kuma aka gudanar da tseren keken mata na farko a kasar Saudiyya, inda suka bai wa mutane da yawa mamaki a kasar ta masu ra'ayin mazan-jiya, musamman a shafukan sada zumunta.
Short presentational grey line
Kasar Saudiyya dai kasa ce da ta ginu kan al'amuran addini, kuma wadannan sauye-sauyen suna alamta yadda kasar ke sauya wa cikin sauri zuwa ga rayuwar da ake yayi a kasashen Turai.
Sai dai wadannan sauye-sauyen da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman yake bullowa da su a kasar, na sanya mutane cikin rudani da jawo ce-ce-ku-ce ba a Saudiyyar ba har ma a sauran kasashen musulmai na duniya.
Ana kallon Saudiyya a matsayin wata jagora ta addinin musulunci, shi ya sa a duk lokacin da ta bullo da wani abu da ba a saba gani ba yake darsa shakku a zukatan wasu.
Source@bbchausa

Post a Comment

0 Comments

ads1