MANYAN HANYOYI GUDA GOMA-(10) NA SAMUN ARZIKI!!!
Arziqi yana da manyan hanyoyin samunsa guda biyu sune;
*A-Hanyar samun Arziqi na Al'ada Wanda ya hada noma da kiyo da kasuwanci da kwadago*.
*B-Hanyar samun arziqi na shari'a,sune wadan nan hanyoyi guda goma,wadanda suka tabbata daga Alqurani da Hadisan Manzon AllahSAW ingantattu*
Dukkan Wanda yake neman Arziqi to wajibine ya bi daya ko wasu daga cikin wadan nan hanyoyi tare da doguwa ga Allah,sannan ya kuma yarda da abinda Allah ya bashi na kason arziqinsa.
Daga Cikin ayoyin da suke bayani a akan arziqi da hanyar samun sun hada da;-
ﻳﻘﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ;(ﻭَﻓِﻲ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ
ﺭِﺯْﻗُﻜُﻢْ ﻭَﻣَﺎ ﺗُﻮﻋَﺪُﻭﻥَ) .
*(Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari)*.
@ﺳﻮﺭﺓ:ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ.
ﻭﻳﻘﻮﻝﺗﻌﺎﻟﻰ (ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻫُﻮَ ﺍﻟﺮَّﺯَّﺍﻕُ ﺫُﻭ ﺍﻟْﻘُﻮَّﺓِ ﺍﻟْﻤَﺘِﻴﻦُ ) .
*(Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi)*.
@ﺳﻮﺭﺓ : ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ
ﻭﻳﻘﻮﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ (ﻫُﻮَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺟَﻌَﻞَ ﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽَ ﺫَﻟُﻮﻟًﺎ ﻓَﺎﻣْﺸُﻮﺍ ﻓِﻲ ﻣَﻨَﺎﻛِﺒِﻬَﺎ ﻭَﻛُﻠُﻮﺍ ﻣِﻦ ﺭِّﺯْﻗِﻪِ ۖ ﻭَﺇِﻟَﻴْﻪِ ﺍﻟﻨُّﺸُﻮﺭُ).
*(Shi, (Allah), Yã sanya muku ƙasa hõrarriya,sai ku tafi cikin sãsanninta,kuma ku ci daga arzikinSa,kuma zuwa gare shi ne tãshin yake)*
@ﺳﻮﺭﺓ : ﺍﻟﻤﻠﻚ .
HANYOYIN ARZIQI NA SHARI'A
1-HANYA TA FARKO
*Yawaita Istighfari*
Kaicon ga Wanda yake neman arziqi amma ya manta da hanya mafi sauki ta samun arziqi a wajen Allah,wato yawaita *ISTIGHFARI*.
ALLAH YANA CEWA
(ﻓَﻘُﻠْﺖُ ﺍﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻭﺍ ﺭَﺑَّﻜُﻢْ ﺇِﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﻏَﻔَّﺎﺭًﺍ
( 10 ) ﻳُﺮْﺳِﻞِ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀَ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢْ ﻣِﺪْﺭَﺍﺭًﺍ( 11 ) ﻭَﻳُﻤْﺪِﺩْﻛُﻢْ ﺑِﺄَﻣْﻮَﺍﻝٍ ﻭَﺑَﻨِﻴﻦَ ﻭَﻳَﺠْﻌَﻞْ ﻟَﻜُﻢْ ﺟَﻨَّﺎﺕٍ ﻭَﻳَﺠْﻌَﻞْ ﻟَﻜُﻢْ ﺃَﻧْﻬَﺎﺭًﺍ ) .
*(Shi na ce,'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku,lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne.""Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga.""Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna)*.
@ﺳﻮﺭﺓ ﻧﻮﺡ ]
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Dukkan Wanda ya lazumci yawaita ISTIGHFARI,to Allah zai Sanya masa mafita a duk lokacin da yake cikin qunci,kuma ya kawo masa farin ciki a duk lokacin da yake cikin damuwa,kuma ya azurta shi daga Inda baya tsammani)*.
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ.
2-HANYA TA BIYU
*Taqwa,wato jin tsoran Allah da kiyaye dokokin Allah,ta hanyar barin abinda yayi hani da aikata abinda yayi umarni*
Allah yana cewa
(وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَيْثُ لَا يَحْتَسِبُ ۚ وَمَن يَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ فَهُوَ حَسْبُهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ بَالِغُ أَمْرِهِ ۚ قَدْ جَعَلَ اللَّهُ لِكُلِّ شَيْءٍ قَدْرًا )
*(Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato.Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma'ishinsa. Lalle Allah Mai iyar da umurninSa ne.Haƙĩƙa Allah Ya sanyama'auni ga dukan kõme)*
@ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻄﻼﻕ
Kuma Allah yana cewa:
(ﻭَﻟَﻮْ ﺃَﻥَّ ﺃَﻫْﻞَ ﺍﻟْﻘُﺮَﻯٰ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﻭَﺍﺗَّﻘَﻮْﺍ ﻟَﻔَﺘَﺤْﻨَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻢ ﺑَﺮَﻛَﺎﺕٍ ﻣِّﻦَ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْض) .
@ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻷﻋﺮﺍﻑ
Jin tsoron Allah hanya CE ta samun arzikin duniya dana lahira,jin tsoran Allah shine mabudin dukkan alkhairi,yawan sabon Allah itace makullin alkhairi kuma mabudin dukkan sharri.
3-HANYA TA UKKU
*Dogaro ga Allah da sallamawa Allah ta hanyar yarda da samu da rashi daga Allah yake,tare da bin hanyoyin da Allah ya sanya na cin nasara da samun arziki sai kuma zuciyarka ta sallama tare da amincewa da yardar akan Allah kadai yake Qaddara samu ko rashi*.
Allah yana cewa;
(وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَيْثُ لَا يَحْتَسِبُ ۚ وَمَن يَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ فَهُوَ حَسْبُهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ بَالِغُ أَمْرِهِ ۚ قَدْ جَعَلَ اللَّهُ لِكُلِّ شَيْءٍ قَدْرًا )
*(Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato. Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to,Allah ne Ma'ishinsa.Lalle Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙĩƙa Allah Ya sanyama'auni ga dukan kõme)*
@ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻄﻼﻕ
Manzon Allah ﷺ yana cewa:
*(Da dai zaku yi dogaro da Allah matuqar dogaro,da Allah ya azurta Ku kamar yadda yake azurta tsuntsu,zai wayi gari cikinsa babu komai,amma yayi yammaci cikinsa a cike)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ
4-HANYA TA HUDU
*Yin aiyukan ibada akan lokaci,wato barin kasala da sakaci game da dukkan aiyukan Ibada,musamman Sallah da Azumin da aiyukan Hajji,kiyaye su da yin su akan lokaci suna janyowa mutum arziqin duniya dana lahira*.
Manzon Allah ﷺ yana cewa:-
(Lallai Allah Ta'ala yana cewa; *{kayi gaggawa wajen kiyaye ibadata da yinta akan lokaci,ni kuma yalwata arzikinta da wadata kuma in yaye maka talauci,.........}*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ
5-HANYA TA BIYAR
*Bibiyar aikin hajji da Umara*
wato yin umar da aikin hajji ga mai wadata akai-akai.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Ku riqa bibiyar aikin hajji da umara akai-akai,domin suna kore Talauci da zunubai kamar yadda wuta take wuta take tsaftace dattin karfe,ita kuma aikin hajji kuma karbabbe baya da wani sakamako sai gidan Aljanna)*.
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ.
6-HANYA TA SHIDA
*Sadar da zuminci*
wato kulawa da dangi na jini da abokai na gari tare da taimaka masu da tallafa masu da kai masu ziyara,wannan hanyace ta samun arziki na duniya da lahira.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Duk wanda yake so Allah ya yalwata arziqinsa,kuma ya tsawaita rayuwarsa,to ya sadar da zumincinsa)*.
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ،
Yalwata arziki yana mufi samu albarka acikin abinda Allah ya azurtaka da shi.
7-HANYA TA BAKWAI
*Addu'a*
wato ka riqa rokon Allah ya baka arziqi mai albarka mai amfani duniy a da lahira,kuma ka roki allah ya kare ka daga talauci da kafirci kamar yadda aka ruwaito acikin addu'o'in Manzon Allah ﷺ yana yin hakan.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Allah yana sauka a kowane dare zuwa samar duniya idan kashi karshe ukkun karshe ya shiga,sai yace; INA MAI KIRANA IN AMSA MASA,INA MAI ROKONA IN BASHI,INA MAI NEMAN GAFARATA INGAFARTA MASA,zai kasance a haka har zuwa fitowar alfijir)*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ
Allah yana cewa;-
(ﻭَﻗَﺎﻝَ ﺭَﺑُّﻜُﻢُ ﺍﺩْﻋُﻮﻧِﻲ ﺃَﺳْﺘَﺠِﺐْ ﻟَﻜُﻢْ)
*(Kuma ubangijinku ya fada; Ku rokeni zan amsa maku)*.
@ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ.
Daga Sahabi Aliyu bn Abi Dhalib R.A,Wani daga cikin bayin da aka rubuta masa fansar kansa,yazo ya sameshi,sai yace,na kasa biyar kudin fansar kaina,ka taimaka min akan hakan,sai yace;
_Zan koya maka wadan su kalmomi wanda Manzon Allah SAW ya koya min su,da kana da bashi wanda ya kai girman dutsai na bashi sai Allah ya hore maka ka biya_ shine kace;
*(ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺍﻛْﻔِﻨِﻲ ﺑِﺤَﻼﻟِﻚَ ﻋَﻦْ ﺣَﺮَﺍﻣِﻚَ ﻭَﺃَﻏْﻨِﻨِﻲ ﺑِﻔَﻀْﻠِﻚَ ﻋَﻤَّﻦْ ﺳِﻮَﺍﻙَ)*
@ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ
8-HANYA TA TAKWAS
*Yin Hijira*
Wato kauracewa sabon Allah da ma'abuta sabon Allah,da kauracewa inda aka hanaka bautar Allah zuwa wajen da Zaka bautawa Allah.
Allah yayi alkawalin taimakonsa da yalwatawa ta arzikinsa ga wanda yayi Hijira saboda Allah.
Allah yana cewa:
(ﻭَﻣَﻦ ﻳُﻬَﺎﺟِﺮْ ﻓِﻲ ﺳَﺒِﻴﻞِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻳَﺠِﺪْ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﻣُﺮَﺍﻏَﻤًﺎ ﻛَﺜِﻴﺮًﺍ ﻭَﺳَﻌَﺔً)
@ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ .
9-HANYA TA TARA
*Yin sammako acikin al'amura*
Wato yin sabko cikin fita neman kudin da kasuwa,kada ka riqa makara fita kasuwa ko shago ko wajen Aiki.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Ya Allah kayi albarka ga Al'ummata cikin sammankon su)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ،
10-HANYA TA GOMA
*Yin sallah da kiyayeta da yinta da kyau kuma acikin lokaci*.
Allah yana cewa;-
(ﻭَﺃْﻣُﺮْ ﺃَﻫْﻠَﻚَ ﺑِﺎﻟﺼَّﻠَﺎﺓِ ﻭَﺍﺻْﻄَﺒِﺮْ ﻋَﻠَﻴْﻬَﺎ ۖ ﻟَﺎ ﻧَﺴْﺄَﻟُﻚَ ﺭِﺯْﻗًﺎ ۖ ﻧَّﺤْﻦُ ﻧَﺮْﺯُﻗُﻚَ ۗ ﻭَﺍﻟْﻌَﺎﻗِﺒَﺔُ ﻟِﻠﺘَّﻘْﻮَﻯٰ).
*(Kuma ka Umarci Iyalinka da sallah kuma koyi hakuri cikin lamarin sallah,bana tambayarka Arziki,mu ne muke azurtaka,kuma karshen al'amari yana ga masu Taqwa)*.
@ﺳﻮﺭﺓ : ﺁﻝ ﻋﻤﺮﺍﻥ ،
ALLAH NE MAFI SANI
*_ﺍﻟﻠَّﻬﻢَّ ﺍﻛْﻔِﻨﻲ ﺑﺤﻼﻟِﻚَ ﻋَﻦ ﺣَﺮَﺍﻣِﻚَ، ﻭَﺍﻏْﻨِﻨﻲ ﺑِﻔَﻀﻠِﻚَ ﻋَﻤَّﻦ ﺳِﻮَﺍﻙَ، ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻲ ﺃَﺳْﺄَﻟُﻚَ ﺍﻟْﻌَﺎﻓِﻴَﺔَ ﻓِﻲ ﺍﻟﺪُّﻧْﻴَﺎ ﻭَﺍﻟْﺂﺧِﺮَﺓِ، ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻲ ﺃَﺳْﺄَﻟُﻚَ ﺍﻟْﻌَﻔْﻮَ ﻭَﺍﻟْﻌَﺎﻓِﻴَﺔَ ﻓِﻲ ﺩِﻳﻨِﻲ ﻭَﺩُﻧْﻴَﺎﻱَ ﻭَﺃَﻫْﻠِﻲ ﻭَﻣَﺎﻟِﻲ_*
0 Comments