SALLAR NEMAN ZABI (ISTIKHAR), HUKUNCINTA DA KUMA YANDA AKE YINTA!!!
.
Sallar Istikhara* Sallace da Akeyi Domin Neman Za6in Ubangiji Game da Wasu Al'amura Biyu da Bawa Yake Bukatar Daya Daga Cikinsu. Sai Yayi Alwala Yayi Sallah Sannan Yayi Wannan Addu'ar Yana Mai Mayarwa Ubangiji Al'amuransa da Yayi Masa Za6in Abinda Yafi Zama Alkhairi._
.
*HUKUNCIN SALLAR ISTIKHARA*
.
Hakika Malamai Sun Hadu Akan Cewa Sallar Istikhara Sunnah ce. Dalili Akan Haka Kuma Shine Hadisi Ingan Tacce Daya Tabbata Daga *Manzon Allah(ﷺ)*._
*{ ﻋَﻦْ ﺟَﺎﺑِﺮٍ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗَﺎﻝَ : ﻛَﺎﻥَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳُﻌَﻠِّﻤُﻨَﺎ ﺍﻻﺳْﺘِﺨَﺎﺭَﺓَ ﻓِﻲ ﺍﻷُﻣُﻮﺭِ ﻛُﻠِّﻬَﺎ ﻛَﻤَﺎ ﻳُﻌَﻠِّﻤُﻨَﺎ ﺍﻟﺴُّﻮﺭَﺓَ ﻣِﻦْ ﺍﻟْﻘُﺮْﺁﻥِ ﻳَﻘُﻮﻝُ : ﺇﺫَﺍ ﻫَﻢَّ ﺃَﺣَﺪُﻛُﻢْ ﺑِﺎﻷَﻣْﺮِ ﻓَﻠْﻴَﺮْﻛَﻊْ ﺭَﻛْﻌَﺘَﻴْﻦِ ﻣِﻦْ ﻏَﻴْﺮِ ﺍﻟْﻔَﺮِﻳﻀَﺔِ ﺛُﻢَّ ﻟِﻴَﻘُﻞْ : ( ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇﻧِّﻲ ﺃَﺳْﺘَﺨِﻴﺮُﻙَ ﺑِﻌِﻠْﻤِﻚَ , ﻭَﺃَﺳْﺘَﻘْﺪِﺭُﻙَ ﺑِﻘُﺪْﺭَﺗِﻚَ.......}*
.
An Kar6o Daga *Jabir (ra)* Yace: *Manzon Allah(ﷺ)* Ya Kasance Yana Koya Mana Istikhara A Cikin Dukkan Al'amuran mu Kamar Yanda Yake Koya Mana Sura Daga Cikin Alqur'ani Yana Cewa: *{Idan Dayanku Yayi Nufin Yin Wani Al'amari, Yayi Raka'a Biyu Bata Farillah ba Sannan Yace: "Ya Allah Ina Neman Za6inka da Iliminka.........."}* (Bukhari)._
*YANDA AKEYIN SALLAR*
1. Alwala:* Zakayi Alwalarka Irin ta Sallah.
2. Niyya:* Sanna Niyya Babu Makawa Sai Kayi Niyyar Wannan Sallah ta Neman Za6i da Zakayi.
3. Sallah:* Sai Kayi Sallah Raka'a Biyu. A Raka'a Ta Farko Za'a Karanta *Qulyã Ayyuhal Kafirun* Bayan An Karanta Fatiha. A Raka'a Ta Biyu Kuma Sai a Karanta *Qul-Huwallahu Ahad*; Itama Bayan Karatun Fatihan.
4. Sallama:* Bayan Kayi Raka'a Biyun Ka, a Karshe Sai ka Sallame Sallar.
5. Addu'a:* Bayan Kammala Sallarka Sai Ka 'Daga Hannunka Sama Kana Mai Qasqantar da Kai Ga Mahaliccinka da Mayar da Al'amuranka Gaba Daya Gareshi Sannan Ka Fara Addu'a.
6. A Farkon Addu'arka Zaka Fara da Yabo ga Ubangiji, Sannan Kayi Salati Ga *Manzon Allah(ﷺ)*. Sannan Salatul Ibrãhimiyya Zakayi Bayan Ka Kammala Salatin Sai Ka Karanto Wannan Addu'ar:
.
*{ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃَﺳﺘﺨﻴﺮُﻙ ﺑﻌِﻠﻤِﻚ، ﻭﺃﺳﺘﻘﺪِﺭُﻙ ﺑﻘُﺪﺭﺗِﻚ، ﻭﺃﺳﺄﻟُﻚ ﻣﻦ ﻓﻀﻠِﻚ، ﻓﺈﻧﻚ ﺗَﻘﺪِﺭُ ﻭﻻ ﺃﻗﺪِﺭُ، ﻭﺗَﻌﻠَﻢُ ﻭﻻ ﺃَﻋﻠَﻢُ، ﻭﺃﻧﺖ ﻋﻠَّﺎﻡُ ﺍﻟﻐُﻴﻮﺏِ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻓﺈﻥ ﻛﻨﺖَُ ﺗَﻌﻠَﻢُ ﻫﺬﺍ ﺍﻷﻣﺮَ - ﺛﻢ ﺗُﺴﻤِّﻴﻪ ﺑﻌﻴﻨِﻪ - ﺧﻴﺮﺍً ﻟﻲ ﻓﻲ ﻋﺎﺟﻞِ ﺃﻣﺮﻱ ﻭﺁﺟﻠِﻪ - ﻗﺎﻝ : ﺃﻭ ﻓﻲ ﺩِﻳﻨﻲ ﻭﻣَﻌﺎﺷﻲ ﻭﻋﺎﻗﺒﺔِ ﺃﻣﺮﻱ - ﻓﺎﻗﺪُﺭْﻩ ﻟﻲ ﻭﻳﺴِّﺮْﻩ ﻟﻲ، ﺛﻢ ﺑﺎﺭِﻙْ ﻟﻲ ﻓﻴﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺇﻥ ﻛﻨﺖَُ ﺗَﻌﻠَﻢُ ﺃﻧّﻪ ﺷﺮٌّ ﻟﻲ ﻓﻲ ﺩِﻳﻨﻲ ﻭﻣَﻌﺎﺷﻲ ﻭﻋﺎﻗﺒﺔِ ﺃﻣﺮﻱ - ﺃﻭ ﻗﺎﻝ : ﻓﻲ ﻋﺎﺟﻞِ ﺃﻣﺮﻱ ﻭﺁﺟﻠِﻪ - ﻓﺎﺻﺮِﻓْﻨﻲ ﻋﻨﻪ، ﻭﺍﻗﺪُﺭْ ﻟﻲَ ﺍﻟﺨﻴﺮَ ﺣﻴﺚُ ﻛﺎﻥ ﺛﻢ ﺭَﺿِّﻨﻲ ﺑﻪ}*
{Allãhumma Inni Astakhiruka Bi Ilmika, Wa Astaqdiru Bi Qudratika, Wa As'aluka Min Fadlika, Fa'innaka Taqdiru Walã Aqdiru, Wa Ta'alamu Walã A'alamu, Wa Anta Allãmul Guyub. Allãhumma Fa'in Kunta Ta'alamu Hãzal Amru (Anan Zaka Fadi Bukatar Taka), Khairan Li Fee Deeni Wa Ma'ãshi, Wa Ãqibati Amri, Faqdurhu Li, Wa Yassirhu Li, Thumma Bãrikli Fihi. Allãhumma Wa'in Kunta Ta''alamu Annahu Sharrun Li Fee Deeni Wa Ma'ãshi, Wa Ãqibati Amri, Fasrifni Anhu, Waqdur Liyal Khaira Haithu Kãna Thumma Raddini Bihi}.
Idan Ka Kammala Wannan Add'ar, Sai Kuma Ka Sake Yin Salatin Annabi Kamar Yanda Kayi Lokacin da Zaka Fara Addu'ar. Shikenan ka Kammala Sallar Istikharanka Sai Kuma Ka Mayar da Al'amuranka Ga Allah Domin Jiran Za6insa.
Sannan ba Mafarki Zakayi ba Kamar Yanda Wasu Suke Fadin, Kawai dai Abinda Yake Alkhairi Zakaji Kafi Natsuwa Dashi.
ABINDA AKESON KIYAYEWA YAYIN SALLAR!!!
1. Mutum Ya Dukufar da Kansa Wurin Neman Za6in Ubangijinsa a Cikin Dukkan Lamuranssa Komai Kankancin Abu.
2. Ka Sanya Yaqini Cewa Lallai Ubangiji Zai Datar Dakai Akan Abinda Shine Mafi Alkhairi a Gareka. Kuma Ta Tattaro Zuciyarka a Lokacin Fara Addu'ar Tare da Tadabburin Abinda Kake Karantawa da Kuma Fahimtar Ma'anarsa.
3. Baya Inganta Mutum Yayi Addu'ar Istkhara Bayan Sallar Farilla. Wajibi ne Sai Kayi Raka'a Biyu ta Nafila ta Musamman Don Yin Wannan Addu'ar.
4. Idan Kanaso Kayi Addu'ar Neman Za6in ne a Bayan Sallolin Nafila Dare da Yini, Kamar Sallar Duha da Makamantasu, Wajibi ne a Farkon Sallar Kayi Niyyar Sallar Istikhara Zakayi. Idan Kayi Niyyar Wata Sallah Bata Istikhara ba, Hakan Bazai Wadatar ba.
5. Idan Akwai Wani Abu da Zai Hanaka Yin Sallah a Wannan Lokacin, Wuce Kamar Mace Mai Haila, Sai a Jira Har Wannan Hailar ta Wuce Sannan Ayi Sallar Istikharan. Idan Kuma Ana tsoron Abinda Ake Neman Za6in Akansa Zai Ku6uce, Sai Ta Nemi Za6in ta Hanyar Yin Addu'ar Kawai Ba Tare da Tayi Sallar ba.
6. Idan Ba'a Haddace Addu'ar ba, Babu Laifi a Dauki Takarda Ana Kallon Addu'ar Har a Kammala Addu'ar. Amma Haddacewar Yafi.
7. Ya Halasta Ayi Addu'ar Istikharan Gabanin Ayi Sallama a Cikin Sallar Wato Bayan Kammala Tahiya, Kamar Yanda ya Hallatta Ayi Addu'ar Bayan Sallame Sallah._
8. Idan Abinda Zai Zama Maslaha a Gareka Bai Bayyana Maka ba, Ya Halasta ka Sake Yin Sallar.
9. Kada Ka Sanya Son Zuciyarka Ya Zamo Shine Zaiyi Hukunci Akan Za6in daka Nema. Domin Tana Yiwuwa Maslaha a Gareka Ya Zamto Bashi Ranka Yakeso ba._
.
_10. Kada ka Kara Kuma Kada Ka RageKomi a Cikin Wannan Addu'ar. Ka tsaya Iyakar Inda Nassi Ya Tsaya Akansa._
.
Wallahu ta'ala A'alam
@Ana muslim
0 Comments